Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Tashar talabijin ta Presstv a nan birnin Tehran ta nakalto Mohammad Abdussalam kakakin kungiyar yana fadar haka a shafinsa na Twitter a ranar Laraba ya kuma kara da cewa karfin sojojin kasar Yemen, musamman bangaren garkuwan sararin samaniyar kasar yana karuwa don fuskantar sojojin Saudiya da kawayenta.
Abdussalam ya kara da cewa kakkabo jirgen leken asiri, kirar kasar Amurka wato ‘Scan Eagle’ da kuma na kirar kasar China 'CH-4' na yaki wadanda garkuwan kare sararin samaniyar kasar Yemen ta yi a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata babbar shaida ce kan wannan.
Tun cikin watan Maris na shekara ta 2015 ne gwamnatin kasar Saudiya tare da kawayenta na kasashen larabawa da kuma Amurka da wasu kasashen Turai suka farwa kasar Yemen da yaki da nufin maida tsohon dan kanzaginsu, Abdurabbu Mansur Hadi kan kujerar shugabancin kasar, amma tare da yardar Allah da kuma jajircewar sojoji da mayakan sa kai na kasar sun kasa kaiwa ga manufofinsu.
342/